A yayin da yake wannan kasa, ana sa ran Mr Li zai tattauna da takwaransa na Krygzstan, Sooronbay Jeenbekov, sannan ya gana da shugaban kasar Almazbek Atambayev inda za su yi musayar ra'ayoyi game da hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannonin tattalin arziki, tsaro, al'adu da sauran fannoni.
Kana a yayin taron kungiyar SCO kuwa, firaministan na kasar Sin zai gabatar da wasu shawarwari da nufin zurfafa hadin gwiwar kungiyar a fannoni da suka shafi harkokin kudi, cinikayya, kimiya da kirkire-kirkire.
Ana sa ran mambobin kungiyar ta SCO su sanar da wasu matakai 38 da aka tsara da nufin bunkasa hadin gwiwa a fannonin sufuri, kimiya da fasaha, samar da kayayyakin more rayuwa da kuma kare muhalli. (Ibrahim)