Ana sa ran firaministan kasar na Sin Li Keqiang zai yi jawabi a taron farko na kwamitin bankin na AIIB sannan akwai jerin ayyuka na bude bankin da zai biyo baya har zuwa ranar litinin.
Bankin na samar da ababen more rayuwa na yankin Asiya wato AIIB da aka kafa shi a hukumance a ranar 25 ga watan Desembar bara a nan birnin Beijing a matsayin cibiyar shi yana da mambobi 57 ya zuwa yanzu.
Ministan kudi na kasar Sin Lou Jiwei ne aka zaba a matsayin shugaban kwamitin bankin sannan Jin Liqun ya zama shugaban bankin na AIIB na farko.
Bikin kaddamar da bankin na AIIB ya zama wani babban cigaba a tarihin tsarin tafiyar da tattalin arziki na duniya in ji Lou Jiwei a hirar shi da manema labarai.