in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban bankin AIIB ya shirya taron manema labaru karo na farko
2016-01-18 14:02:04 cri
Bankin saka jari game da muhimman ababen more rayuwa na kasashen Asiya wato AIIB ya shirya taron manema labaru karo na farko a nan birnin Beijing, inda shugaban banki na farko Jin Liqun ya halarci taron, gami da amsa tambayoyin da manema labaru suka yi masa.

An zabi Jin Liqun a matsayin shugaban bankin na farko yayin taron kafa kwamitin bankin na AIIB da aka shirya a ranar 16 ga wata. A yayin taron na tsawon mintoci 30, Jin Liqun ya amsa tambayoyi 15 masu muhimmanci ciki har da batun 'yancin kada kuri'a, da tsarin sa ido, da shigar da sabbin mambobi da yin amfani da asusun musamman da tattara jari daga hukumomin daban daban, da daukar kwararru da magance hadarurruka da dai sauransu.

A jawabinsa Jin Liqun ya bayyana cewa, ya zuwa ranar 17 ga wata, akwai kasashe mambobi 30 da suka amince da yarjejeniyar bankin AIIB, kuma jarin da wadannan kasashe suka zuba a bankin ya kai kashi 74 cikin 100.

Mr. Jin dai ya taba rike da mukamin mataimakin ministan kudi na kasar Sin, kuma mataimakin shugaban bankin raya Asiya, da shugaba mai kula da sanya ido kan harkokin kamfanin saka jari na Sin, kana da shugaban kamfanin hada-hadar kudi na kasa da kasa na Sin, kuma ya kware sosai a fannin shugabanci da tafiyar da ayyukan gudanarwa a hukumomin gwamnatin Sin da na kasa da kasa da sauran hukumomi masu zaman kansu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China