in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya halarci bikin kafa majalisar zartaswa ta bankin AIIB
2016-01-17 14:03:50 cri
A ran 16 ga wata da yamma, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci bikin kafa majalisar zartaswa ta bankin zuba jari kan ababen more rayuwa na Asiya, watau AIIB da aka yi a nan birnin Beijing na kasar Sin, inda ya nuna fatansa guda uku dangane da yadda za a gudanar da ayyukan bankin.

Da farko, ya ce, ya kamata a ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa gaba a kan gina ababen more rayuwa da kuma habaka hadin gwiwar dake tsakanin shiyya-shiyya kan harkokin tattalin arziki bisa shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, bankin AIIB zai yi hadin gwiwa da bankin raya Asiya na ADB da dai sauran hukumomin da abin ya shafa domin neman ci gaba tare, haka kuma, ana maraba da halartar sauran hukumomin kasa da kasa da abin ya shafa domin karfafa ayyukanmu yadda ya kamata.

Na biyu, ana fatan za a iya inganta hadin gwiwar duniya a fannin masana'antu, domin habaka bukatun kasa da kasa a wannan fanni. Haka kuma, dangane da bukatun mambobin kasashe masu tasowa wajen neman bunkasuwar masana'antu da birane, ya kamata a fidda dabaru na yin amfani da fasahohin zamani, yayin da ake ba tare da kashe kudade sosai ba, domin nuna goyon baya gare su yadda ya kamata. Kaza lika, ya kamata a habaka sabbin hanyoyin yin hadin gwiwa cikin himma da kwazo, ta yadda za a iya karfafa kwarewar kasa da kasa wajen neman bunkasuwa da kansu, da kuma zurfafa bunkasuwar sana'o'i daban daban cikin kasashen yadda ya kamata.

Na uku, shi ne, ana fatan sabunta tsarin yin hadin gwiwa, yayin da ake mai da hankali kan bukatun abokan kasashen a lokacin da ake yin hadin gwiwa tare da su, da kuma karfafa shawarwarin dake tsakaninmu, ta yadda za a iya samar da sabbin damammaki bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa da kuma a tsakanin kasashe masu tasowa da ke samun ci gaba, domin samun sakamako mafi karfi ta fuskar neman ci gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China