"Muna da wani shirin rijistan masu zabe dake gudana a dukkan fadin kasar, ina gayyatarku wajen halarta da kuma samun katin zabenku domin zabuka masu zuwa", in ji shugaban kasar Congo a yayin wani taron gangami a Kasindi, wani yankin dake kan iyaka da Uganda.
Joseph Kabila ya yi kuma kira ga al'ummar Arewacin Kivu da su runguna manufar tabbatar da zaman lafiya domin cimma nasara kan ayyukan ci gaban ababen more rayuwa da kuma maido da ikon gwamnati a wannan bangare na kasar.
Tun 'yan shekaru da dama, yankuna da kauyukan Arewacin Kivu suka kasance masu fama da hare haren 'yan tawayen Uganda na kungiyar ADF. (Maman Ada)