Wata muhimmiyar takarda da ma'aikatar kula da albarkatun man kasar ta fitar a karshen mako, ta bayyana cewa, sabuwar hukumar za ta hade dukkan ayyukan hukumomin da ke kula da albarkatun man kasar, sannan kuma za ta kunshi wasu sabbin ayyuka da ba a sanya su a baya ba.(Vanguard)
Kungiyar tsagerun Niger Delta mai suna Niger Delta Avengers ta shaidawa shugabannin yankin a jiya Lahadi cewa, kungiyar ta kai hare-hare kan na'urorin mai da ke yankin, duk da tattaunawar zaman lafiya da dattawan yankin ke yi da gwamnatin tarayyar Najeriya, amma hakan ba laifinta ba.
Kungiyar ta ce, babu abin da za ta yi, illa ta gurgunta na'urorin man da ke yankin, saboda zargin gwamnati da kin martaba sharuddan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka cimma kafin su kira tattaunawa da shugabanni da sarakunan gargajiya da ke yankin, a wani mataki na kawo karshen rikicin da ke faruwa a yankin.(The Punch)