in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin ladabtarwa na JKS ya sha alwashin tabbatar da bin ka'idojin jam'iyya
2016-11-02 09:50:31 cri

Kwamitin ladabtarwa wato CCDI na JKS ya sha alwashin tabbatar da matsa kaimi, wajen ganin ana bin dokokin gudanarwar jam'iyyar kwaminis sau da kafa.

Kwamitin na CCDI ya alkawarta hakan ne a jiya Talata, yayin taron nazari da lalubo hanyoyin aiwatar da muradun da aka cimma, a yayin taro na 6 na kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin wato JKS karo na 18.

Wata sanarwar bayan taron da aka fitar, ta bayyana cewa, a yayin zaman, an fitar da wasu kundin bayanai biyu, masu taken "dabi'un rayuwar jam'iyya a sabon yanayin da ake ciki", da kuma "ka'idojin sanya ido game da ayyukan jam'iyya".

Taron wanda sakataren kwamitin na CCDI Wang Qishan ya jagoranta, ya kuma ja hankalin mambobinsa da su zamo abun misali, wajen aiwatar da sabbin manufofin dake kunshe cikin kundin bayanan biyu, tare da daukar dukkanin matakan da suka dace, na warware matsalolin da jam'iyyar ke fuskanta. (Saminu Al-hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China