Tsohon babban sakataren kwamitin kungiyar tarayyar turai EU, kuma Professor na kwalejin nahiyar Turai Gerhard Stahl, ya bayyana cewa, muhimman takardu da sanarwa da aka gabatar sun bayyana cewa, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, tana kokarin dacewa da sauyin yanayi da ake ciki, da kasancewarta jam'iyya ta zamani, hakan ya shaida cewa, jam'iyyar tana da cikakkiyar niyyar yaki da cin hanci. Idan ana son raya tattalin arziki, tilas ne a yi yaki da cin hanci da gudanar da harkoki bisa dokoki.
Shugaban kwamitin harkokin duniya na Islamabad na kasar Pakistan Khaled Mahmoud, ya bayyana cewa, kara sa ido ga gudanar da harkokin jam'iyyar shi ne mihimmin mataki da JKS take aiwatarwa, ta haka ne za a kara gudanar da ayyukan gwamnatin kasar yadda ya kamata, da sa kaimi ga jama'a da su kara yin imani ga JKS. Kana wannan zai sa kaimi ga yin kwaskwarima a dukkan fannoni da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, ta yadda za a amfanawa dukkan duniya baki daya. (Zainab)