Wani karin adadin 'yan gudun hijira dubu 185 sun tsere tun bayan barkewar sabbin tashe tashen hankali a farkon watan Yuli a cikin wannan kasa, in ji kakakin.
Yawancin sabbin mutanen da suka zo sun ratsa kan iyaka domin shiga Uganda, amma kuma an gano wani karin zuwan mutane a yankin Gambella na kasar Habasha a makon da ya gabata, wasu mutanen sun kama hanyar zuwa Kenya, RDC-Congo da Afrika ta Tsakiya. Wadannan kasashe, abin nuna yabo, shi ne sun bar kan iyakokinsu bude domin sabbin 'yan gudun hijirar, in ji mista Dobbs.
A cewar HCR, yawancin wadannan mutanen da suka tsere daga Sudan ta Kudu, mata ne da yara. Daga cikinsu, akwai wadanda suka tsira daga tashe tashen hankali, ayyukan cin zarafin mata da fyade, yara da aka raba da iyayensu ko masu tafiye tafiye su kadai, da nakasassu, da tsofaffi, da kuma mutanen da ke bukatar jinya cikin gaggawa. (Maman Ada)