in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabbin tashe tashen hankali sun barke tsakanin dakarun jahohin Somaliya duk da yarjejeniyar tsagaita wuta
2016-11-06 12:57:36 cri
Tashe tashen hankali sun barke tsakanin dakarun jahohin Somaliya na Puntland da na Galmudug a birnin Galkayo dake tsakiyar kasar a wannan mako duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, in ji cibiyar kula da harkokin jin kai ta MDD (OCHA) a ranar Asabar.

Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a ranar 1 ga watan Nuwamba, wasu sabbin yake yake sun barke a ranar 2 ga watan Nuwamba kuma hali ya tsananta a Galkayo, inda kowane bangare ya tsaya kan bakansa, in ji OCHA.

Har yanzu ba a san adadin mutanen da suka mutu ba a cikin tashe tashen hankalin tun a ranar 2 ga watan Nuwamban.

Shugabannin Galmudug da na Puntland sun sanar a farkon mako da cimma wata yarjejeniyar tsagaita wuta a karkashin jagorancin daular kasashen Larabawa. Haka kuma, bangarorin biyu na shirin gudanar da shawarwari a ranar 20 ga watan Nuwamba domin tattauna batun aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya.

Kimanin mutane dubu 40 da suka kaura a Galkayo ne kuma dole zasu sake barin birnin. Yawanci daga cikinsu sun tafi yin zaman rayuwa a cikin kauyuka dake kewayen Galkayo. An gurgunta ayyukan kasuwanci da na noma, haka kuma fiye da dalibai dubu 20 basu iya zuwa makaranta, in ji OCHA, tare da jaddada cewa kungiyoyin bada agaji an tilasta musu takaita kai da kawo ma'aikatansu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China