in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mayakan Al-Shabaab 8 da wasu sojoji 4 yayin wani bata kashi a Somaliya
2016-10-31 10:06:33 cri
Rahotanni na cewa sojoji da mayakan kungiyar Al-Shabaab sun yi wani dauki ba dadi a jiya Lahadi, a wani wuri dake kusa da garin Baidoa a jihar kudu maso yammacin kasar Somalia, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar dakarun kungiyar 8 da kuma sojoji 4, baya ga wasu karin sojojin 6 da suka samu raunuka.

Da yake karin haske game da aukuwar lamarin, ministan ma'aikatar watsa labarai a jihar ta kudu maso yamma Ugaas Hassan, ya shaidawa mane ma labarai cewa dakarun kungiyar ta Al-Shabaab sun yiwa wani sansanin sojojin kasar kwantan bauna ne, kafin sojojin su maida martani, lamarin da ya haifar da musayar wuta da kuma rasa rayuka.

Sai dai a hannu guda, ministan ya musanta ikirarin da kungiyar ta Al-Shabaab ta yi, cewa ta kwace wani yankin dake kudu maso yammacin kasar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China