in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan bindiga sun hallaka wani babban jami'in tsaron a birnin Mogadishu
2016-10-25 19:08:30 cri
Wasu 'yan bindiga da ake zargin mayakan kungiyar Al-Shabaab ne, sun hallaka wani babban jami'in tsaron kasar a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar.

Kakakin hukumar tsaron cikin gidan kasar Abdikamil Moalim Shukri, shi ne ya tabbatar da hakan a Talatar nan, yana mai cewa maharan sun harbe Abdiaziz Araye ne da bindiga jiya da almuru, sa'an nan kuma suka tsere.

Kafin rasuwar sa Mr. Araye, jami'in tsaron farin kaya ne dake aiki a gundumar Waberi.

Yanzu haka dai jami'an tsaro na ci gaba da farautar wadannan 'yan bindiga.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China