in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta fara farautar masu aikata laifin cin hanci
2016-11-11 09:24:54 cri

Hukumar ladaftarwa ta kwamitin tsakiya na JKS ta tura tagawar masu yaki da cin hanci da rashawa zuwa larduna da yankunan kasar guda 19, domin zakulo wadanda ake zargi da aikata laifukan cin hanci da karbar rashawa.

Wata sanarwa da hukumar ta raba wa manema labarai ta bayyana cewa, wannan bincike wanda shi ne na uku a wannan shekara, zai mayar da hankali kan sassan jam'iyyar guda 27 a wadannan wurare. Bayan shekaru biyar ne dai aka sanya batun yaki da cin hancin a cikin kundin tsarin mulkin jam'iyya.

A ranar 15 ga wannan watan ne za a tura tawagogin yaki da cin hanci zuwa dukkan hukumomin kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China