in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na goyon bayan Tanzaniya a kokarinta na yaki da cin hanci
2015-06-17 09:39:37 cri

Gwamnatin kasar Sin a ranar Talatan nan ta ba da gudunmuwar na'urorin sadarwa na kimanin kudin dalar Amurka miliyan 1.5 ga ayyukan sa ido da Tanzaniya take yi a kokarinta na yaki da cin hanci.

Edward Hoseah, babban darakta na hukumar hana da yaki da cin hanci ta Tanzaniya ya ce, gudunmuwar na'urorin wata alama ne da ta bayyana a fili irin zumuncin kusa dake tsakanin kasashen biyu.

Ya ce, na'urorin sun hada da kamfutocin na dorawa a kan teburi 162, kamfutocin hannu 13, na'urorin buga takardu 20, na'urorin tantance takardu 90, da kuma na'urorin sadarwar 162, da da sauran bukatu na kumfutoci 4.

A cewar jami'in, yaki da cin hanci na bukatar yin shawara cikin sauri tare da amfani da kayayyakin sadarwa na zamani da za su tafi ta fasahar gudanar masu cin hanci ta ko wane hali.

Da yake magana a takaice kafin ya mika kayayyakin, jakadan kasar Sin dake Tanzaniya Lu Youqing ya ce, kasashen Tanzaniya da Sin suna aiki tare don inganta ayyukan yaki da cin hanci a duniya. Ya ce, yaki da cin hanci yana da wahala, amma ya ba da tabbacin cewa, gwamnatin kasar Sin da hukumar yaki da cin hanci ta kasar Tanzaniyar za su yi aiki tare. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China