in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ladaftar da jami'ai 4,417 game da laifukan almubazzaranci
2016-08-23 10:28:26 cri

A cikin watan Yulin da ya gabata, hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ta jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin JKS, ta ladaftar da jami'ai da yawan su ya kai 4,417, bisa laifin keta dokar tsimin kudaden hukuma.

Hukumar ta CCDI ta ce, ta samu jami'an da hannu cikin laifuka 3,044, wadanda suka hada da ba da kudin kyauta ba bisa ka'ida ba, wanda shi ne laifi da ya fi yawan aukuwa. Sauran sun hada da karba ko ba da kyautuka ta hanyar da ba ta dace ba, da kuma facaka da kudin gwamnati. Kaza lika an samu wasu da laifin amfani da motocin hukuma ba bisa ka'ida ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China