in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar wakilan Sin ta halarci taron kasashen da suka daddale yarjejeniyar yaki da cin hanci da rashawa ta MDD karo na 6
2015-11-04 13:59:19 cri
A ranar Litinin ne aka kaddamar da taron kasashen da suka daddale yarjejeniyar yaki da cin hanci da rashawa ta MDD karo na 6 a birnin St. Petersburg dake kasar Rasha, taron da ya samu halartar wakilai daga kasashe fiye da 160 da hukumomin kasa da kasa fiye da 10. Mataimakin shugaban hukumar yaki da hanci da rashawa ta kasar Sin kuma shugaban hukumar hadin gwiwa tare da ketare ta kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Liu Jianchao shi ne ya jagoranci tawagar kasar Sin a taron inda ya bayyana matsayin Sin a muhawarar da aka gudanar a taron.

Liu Jianchao ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru biyu da suka gabata, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kara daukar matakan yaki da cin hanci da rashawa, lamarin da ya haifar da kyakkyawan sakamako.

Bugu da kari, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta shigar da matakan neman wadanda suka tsere zuwa kasashen waje a sakamakon aikata laifin cin hanci da rashawa da kuma dukiyar da suka sata a cikin ayyukan yaki da cin hanci da rashawa na jam'iyyar.

Haka zalika kuma, Liu Jianchao ya jaddada cewa, a halin yanzu kasar Sin ta ba da muhimmanci wajen kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa don yaki da cin hanci da rashawa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China