in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron karawa juna sani na 'yan majalisar dokokin Asiya da Afirka a birnin Beijing
2016-09-19 10:20:44 cri
A jiya Lahadi 18 ga watan nan ne aka yi bikin budewar taron karawa juna sani na 'yan majalissar dokokin kasashen Asiya da Afirka a birnin Beijing na kasar Sin. Taken taron dai shi ne "kyautata ayyukan majalisun dokoki, domin ba da taimako wajen cimma burin neman dauwamammen ci gaba a duniya". Kana majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da kungiyar majalissu ta kasa da kasa wato IPU ne suka shirya da kuma gudanar da wannan taro cikin hadin gwiwa.

Mataimakin shugaba, kana babban sakataren zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wang Chen ya halarci bikin bude taro na 'yan majalissar dokokin kasashen Asiya da Afirka, inda ya kuma bayyana cewa, neman ci gaba nauyi ne na kasa da kasa, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba yin alkawari a madadin kasar Sin a yayin taron kolin ci gaba na MDD cewa, kasar Sin tana fatan ba da gudummawa da gudanar da hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya wajen tabbatar da aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba.

Haka kuma, taron karawa juna sanin na 'yan majalisar dokokin na hadin gwiwa zai ba da taimako matuka wajen karfafa mu'amala a tsakanin majalissun kasashe masu tasowa, ta yadda za a kyautata ayyukan da suka shafi hakan, yayin da samar da sabbin damammaki wajen cimma burin na neman samun dauwamammen ci gaba, lamarin zai kuma tallafawa al'ummomin kasa da kasa.

Shi ya sa, ya kamata majalissun kasashe masu tasowa su karfafa mu'amalar dake tsakaninsu a fannonin kafa dokoki, da kuma sa ido kan harkokin da suka jibanci haka da sauransu, ta yadda za a samar da yanayi mai kyau game da tabbatar da dauwanammen ci gaban duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China