in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin zai kai ziyara a kasashen Ecuador, Peru, da kuma Chile
2016-11-09 19:29:15 cri
A yau Laraba 9 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin, Lu Kang ya shelanta cewa, bisa goron gayyatar da takwarorinsa na kasashen Ecuador da Peru da kuma Chile suka ba shi, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyara a wadannan kasashen uku tsakanin ranekun 17 zuwa 23 ga watan nan.

Ana sa ran kuma bisa goron gayyatar shugaban kasar Peru, shugaba Xi zai halarci kwarya kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 24 a birnin Lima na kasar ta Peru tsakanin ranekun 19 zuwa 20 ga watan. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China