in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin kudin shiga na Sin ta fuskar yawon shakawata ya kai RMB biliyan dubu 2.9 a watanni tara na farkon wannan shekara
2016-11-05 13:19:55 cri
Bisa labarin da aka samu a jiya Jumma'a, an ce, cikin watanni tara na shekarar bana, adadin mutanen dake kasar Sin wadanda suka yi yawon shakatawa a kasar ya kai miliyan 3360, yayin da mutane kimanin miliyan 194 da suka zo daga ketare sun yi yawon shakawata a kasar Sin a shekarar bana, lamarin da ya sa, gaba daya an samu kudin shiga RMB biliyan dubu 2.9 ta fuskar wannan fanni cikin wadannan watanni tara da suka gataba, kuma adadin da suka karu da kashi 11 bisa 100, da kashi 13.5 bisa 100 da kuma kashi 3.7 bisa 100 idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar da ta wuce.

Haka kuma, a lokacin hutu na kwanaki bakwai domin taya murnar ranar kafuwar kasar wanda ya fara daga ranar 1 ga watan Oktoba, gaba daya akwai mutane miliyan 593 da suka je yawon shakatawa a kasar, adadin da ya karu da kashi 12.8 bisa 100, kuma gada daya an samu kudin shiga na RMB biliyan 482.2, adadin da ya karu da kashi 14.4 bisa 100 idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar da ta gabata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China