in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta dauki niyyar mayar da aikin kona shara kan girmama muhalli
2016-11-07 10:45:32 cri
Hukumomin kasar Sin sun fitar da wani kundin bada jagoranci kan kula da bolar birane ta hanyar konasu, domin samun daidaito ga karuwar bolar gidaje a cikin birane.

Wannan kundi da aka fitar tare da ma'aikatun gwamnati guda hudu, da suka hada da ma'aikatar gidaje da gine ginen birane da kauyuka da kwamitin kula da cigaba da gyare gyare, sun dauki niyyar karfafa dokoki kan zabin wurare domin kafa injunan kone konen sharar gidaje.

Wadannan gine gine dole su amsa manyan ka'idoji da kuma tabbatar da giramama mullahi. A yanzu ayyukan da ba su amsa wadannan ka'adoji za a rufe su, a cewar wannan kundi.

Haka kuma kundin na tilasta masu gabatar da dokoki da su aiwatar da tsarin bin diddigi masu hannu da shirye shiryen gaggawa da kuma cimma nargatattun matakai domin sanya ido ga duk wata yiyuwar gurbata muhalli.

Ana neman rage shakku da jama'a da suke nuna ga injunan kone konen shara ta yadda za a samu zaman daidaituwa tare da da gine-gine masu amfani da makamashi mai tsabta, wasannin motsa jiki, da na shakatawa, har ma gabatar da ruwa, da samar da na'urorin dumama wuri da wutar lantarki ga mazauna wuraren cikin rahusa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China