in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da shugaban kasar Guinea
2016-11-01 21:41:23 cri
A yau Talata 1 ga watan Nuwamba, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaba Alpha Conde na kasar Guinea wanda yake yin ziyarar aiki a nan kasar Sin.

Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin tana son hada kai tare da kasar Guinea wajen karfafa dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani sabon mataki. Bugu da kari, bangaren Sin yana taya wa kasar Guinea murnar fita daga mummunan halin da annobar Ebola ta haifar mata. Li ya kara da cewa, kasar Sin tana son kara yin hadin gwiwa da kasar Guinea a fannonin kiwon lafiya domin tinkarar annoba mai tsanani matuka tare.

A nasa bangaren, Mr. Conde ya ce, kasar Guinea tana yaba wa manufofin sada zumunta a zahiri da kasashen Afirka da Sin suke aiwatarwa. Kuma yana fatan kara yin hadin gwiwa da Sin wajen bunkasa kayayyakin more rayuwar al'umma da aikin gona da makamantansu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China