in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mali: 'Yan adawa sun yi jerin gwano domin dawowar tsohon shugaban kasar Amadou Toumani Toure
2016-10-02 13:02:37 cri
Jam'iyyun adawa na kasar Mali sun yi jerin gwano a ranar Asabar a birnin Bamako domin bukatar dawowar tsohon shugaban kasar Amadou Toumani Toure dake gudun hijira a Senegal tun bayan da aka yi masa yuyin mulki a shekarar 2012.

Masu zanga zangar da aka kiyasta yawansu kusan dubu 100 a cewar wadanda suka shirya jerin gwanon amma kuma dubu biyu a cewar 'yan sanda, sun yi jerin gwano daga dandalin 'yanci zuwa dandalin cibiyar 'yan kwadago tare da wucewa ta dandamalin samun 'yancin kai.

Sun yi allawadai kan yadda gwamnti take tafiyar da harkokin kasa da dokar zabe, tare da neman ganin an shirya shawarwarin kasa domin cigaban shirin zaman lafiya, da kuma baiwa 'yan adawa damar yin amfani da talabijin din kasa.

Shugaban 'yan adawa, dan majalisa Soumaila Cisse, ya soki gwamnati sosai. Tun yau da shekaru uku an rasa tudun dafawa a kasar Mali. An manta da cewa Kidal dake arewacin kasar wani yanki ne na kasar Mali. Hakan ba ya daidai ga arewacin Mali, da kuma tsakiyar Mali. Kasar Mali nada gwamnatin dake tangal tangal. Ba a san inda za a sanya gaba ba, in ji shugaban 'yan adawa domin bayyana dalilinsa na ganin an gudanar da shawrwarin kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China