in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon yayi kira ga bangarori daban daban dasu aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya cikin sauri a Mali
2016-09-24 13:10:39 cri
Sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon ya gayyaci a ranar Jumma'a dukkan bangarorin da abin ya shafa dasu aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da sasantawa cikin sauri a kasar Mali.

Ina kira ga kungiyoyi masu makamai dasu daina janyo fito na fito kana dukkan bangarori su ajiye muradunsu na gajeren lokaci a gefe guda domin su aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a kasar Mali, in ji mista Ban a yayin wani taron ministoci kan wannan yarjejeniya, da aka shirya a dab da babban taron MDD a birnin New York, wanda ya samu halartar shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita.

Bunkasa zaman lafiya da zaman karko a kasar Mali shi ne muhimman abu na farko ga al'ummarta, ga yankin da ma duniya, in ji mista Ban tare da jaddada cewa duk wasu nasarorin da aka samu tun lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar, nasarori ne dake da rauni, kuma ana ganin har yanzu akwai tashe tashen hankali dake take yarjejeniyar tsagaita wuta.

Rashin tsaro na shafar al'ummomi wajen samun agajin abinci cikin gaggawa da suke bukata, musammun ma mutane rabin miliyan, wadanda suka hada da yara dubu 180 dake fama da karancin abinci mai gina jiki mai tsanani, in ji shugaban MDD.

Taron ministocin ya shafi mambobin tawagar shiga tsakani ta kasa da kasa dake kunshe da Aljeriya, Burkina Faso, ECOWAS, Mauritaniya, MDD, Nijar, Kungiyar dangantakar musulunci, Chadi, AU da kuma EU, da kuma mambobin kwamitin sulhu. Haka kuma kasashen dake samar da dakaru da kuma 'yan sanda ga tawagar MINUSMA sun halarci wannan haduwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China