in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da hari kan jami'an wanzar da zaman lafiya a Mali
2016-10-04 11:58:06 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yi tir da jerin hare haren da aka kaddamar kan wasu dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD dake aiki a kasar Mali, lamarin da ya sabbaba kisan soji daya dan asalin kasar Chadi, tare da jikkata wasu dakarun su 8.

Cikin wata sanarwa da kakakin sa ya fitar, Ban Ki Moon ya ce an kaddamar da hare hare har sau 4 kan dakarun tawagar ta MINUSMA, da ma wasu kayayyakin aikin su a yankunan Aguelhok da Kidal dake arewacin Mali.

Ya ce kaddamar da hari kan dakarun wanzar da zaman lafiya laifin yaki ne, don haka ya bukaci a gaggauta damke wadanda suka aikata wannan ta'asa, da kuma gurfanar da su gaban shari'a.

Tawagar MINUSMA dai na shan fama da hare haren ta'addanci a Mali, inda ya zuwa yanzu ta yi rashin jami'ai sama da 60, wanda hakan ya zarta adadin da sauran tawagogin MDD suka rasa a sauran wurare da suke gudanar da ayyuka. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China