in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya bukaci a aiwatar da manufofin gyare-gyare kamar yadda aka tsara
2016-11-01 19:22:30 cri
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi kira da a aiwatar da manufofin gyare-gyare kamar yadda aka tsara.

Shugaba Xi wanda ya yi wannan kiran a yau Talata, yayin taron kwamitin yin gyare-gyare karo na 29 wanda yake shugabanta, ya bukaci jami'ai da su bi sanarwar bayan taron cikakken zaman taro na 6 na kwamitin tsakiyar JKS na 18 da aka kammala ba da dadewa ba wajen aiwatar da gyare-gyaren sau da kafa.

Haka kuma a yayin taron, an amince da dokoki da tsare-tsare game da inganta aikin gona ba tare da gurbata muhalli ba, da matakan kare muhalli, da sabbin dokokin kananan kotuna, da bullo da tsarin samar da rance. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China