in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Guinea
2016-11-02 20:36:56 cri

 

Yau Laraba shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Guinea Alpha Condé a nan birnin Beijing.

A jawabinsa yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Guinea ita ce kasa ta farko a cikin kasashen da ke yankin kudu da Hamadar Sahara da ta kulla huldar diplomasiyya tare da sabuwar kasar Sin. A cikin shekaru 57 da suka gabata, ko da yaushe kasashen biyu su kan nuna sahihanci da sada zumunta ga juna, da zaman daidai wa daida a tsakaninsu, tare da nuna fahimta da goyon baya ga juna a kan muhimman lamuran da suka shafi muradun juna da kuma manyan batutuwan da ke jawo hankulansu.

Bugu da kari, Shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata kasashen Sin da Guinea su nace ga raya dangantakar da ke tsakaninsu bisa hangen nesa da manyan tsare-tsare, da inganta cudanya da hadin gwiwa a tsakanin gwamnatoci, jam'iyyun da ke kan karagar mulkin kasashen, hukumomin tsara dokoki, gwamnatocin jihohin kasashen biyu, a kokarin aza harsashi mai inganci ta fuskar siyasa. Kasar Sin na marawa Guinea baya wajen neman samun hanyar ci gaba da ta dace da halin da kasar ke ciki.

A nasa bangaren kuma, Shugaba Condé ya bayyana cewa, kasarsa tana godiya ga kasar Sin bisa goyon bayan da take nuna mata, ciki har da taimakon da Sin ta bai wa gwamnati da jama'ar kasar Guinea wajen yaki da cutar Ebola. Kasar Guiena na son inganta hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannonin da suka shafi albarkatu, makamashi, kimiyya da fasaha, ayyukan noma, samar da ruwa da wutar lantarki, muhimman ababen more rayuwa, da kuma gina tashoshin jiragen ruwa, da kara cudanya tare da Sin a fannin gudanar da harkokin kasa.

Shugaba Condé ya kara da cewa, kasarsa na yabawa manufofin da kasar Sin take aiwatarwa game da Afirka, kuma tana dukufa wajen shiga ayyukan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka bisa tsarin "manyan shirye-shirye goma na hadin gwiwa" da shugaba Xi ya gabatar a yayin taron kolin FOCAC da aka gudanar a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu. Haka kuma Guinea na da aniyar zama kawar kasar Sin a nahiyar Afirka. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China