Ya ce yayin taron kungiyar BRICS da ya gudana a birnin Goa na kasar Indiya, shugaba Xi ya gabatar da wasu kudurori 5 wadanda ka iya tallafawa kungiyar, musamman ma a yanayi na matsin tattalin arziki.
Cikin jawabin da ya gabatar, shugaban na Sin ya ce ya dace a bude kofa ga juna, a kuma fidda managartan tsare tsaren ci gaban hadin gwiwa, a kuma fuskanci kalubalen da suka fi fuskantar duniya a yanzu. Sauran kudurorin sun hada da aiwatar manufofi bisa gaskiya da adalci tsakanin kasashen duniya, tare da inganta hadin kai tsakanin hukumomin kasa da kasa.
Ministan harkokin wajen na Sin ya kara da cewa, wannan ziyara ta shugaba Xi, ta tabbatar da manufar kasar Sin a fannin karfafa kawance na diflomasiyya, mai kunshe da gaskiya da adalci, da mutunta juna tsakanin kasashen makwabta, ta hanyar karfafa dangantakar da ke ci gaba da wanzuwa. Har wa yau, za ta dada daidaita tsarin aiwatar da manufar nan ta ziri daya da hanya daya, ta yadda za ta dace da manufofin ci gaban kasashen dake ciki, tare da fadada hadin kai tsakanin kasuwannin kasashe masu tasowa. (Saminu Alhassan)