An bayyana a cikin sakon cewa, wannan aiki na harba sabuwar rokar ya maye gurbin tsoffin fasahohin dake kushe a nau'o'in rokoki kirar kasar Sin. Aikin mai wuyar gaske, wanda ya shafi fasahohin ci gaba masu sarkakiya, ya nuna matsayin kolin da kasar Sin ta cimma ta fuskar fasahar roka. Kaza lika kuma yadda aka harba sabon nau'in rokar cikin nasara, ya sa kasar Sin tabbatar da samun fasahar kera wani nau'in roka mai amfani da sabon nau'in makamashi dake da matukar karfin daukar kaya, kuma mai aiki ba tare da gurbata muhalli ba.
Har wa yau hakan ya tabbatar da matsayin kasar Sin na kasancewa a kan gaba a duniya, a fannin kera roka mai daukar kaya, kuma ya shaida cewa kasar ta kai ga mallakar fasahar ci gaba ta fuskar zirga-zirga a sararin samaniya. Bugu da kari, ci gaban ya aza harsashi na musamman a fannin fasahohi, da yunkurin samar da rokoki nau'o'i daban daban a kasar Sin.(Bello Wang)