in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kara bude kofa ga kasuwannin duniya
2016-11-01 10:54:30 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin mista Wang Yi da takwaransa na kasar Faransa Jean-Marc Ayrault, sun gana da manema labaru a jiya Litinin a nan birnin Beijing, inda Mr. Wang ya mayar da martani ga wasu zarge zarge, dangane da muhallin zuba jari a kasar Sin, da aikin zuba jari ga kasashen waje da wasu kamfanonin kasar Sin suke yi.

A cewar mista Wang, a shekarun baya bayan nan kasar Sin da kasashen waje suna kokarin zuba wa juna jari, matakin da ya zamo hanya mai kyau da ake bi wajen gudanar da hadin gwiwa mai amfani ga juna.

A fannin zuba jari ga kasashen waje, kasar Sin ta kan karfafa wa manyan kamfanonin ta gwiwar bin ka'idojin kasuwanci, domin gudanar da hadin gwiwa da kasashen dake da niyyar samun jarin kasar Sin.

A nasu bangaren, kamfanonin kasar Sin, in ji ministan kasar, na bin dokokin kasashen da rassansu ke ciki, tare da girmama al'adun al'ummar wurin. Saboda haka a cewar ministan, ya yi imanin za a ga ci gaban ayyukan kamfanonin, gami da samar da sakamako da zai amfani dukkan bangarori.

Ban da haka, ministan ya yi magana kan batun zuba jari ga kasar Sin, inda ya ce manufar kasar Sin tana da tabbas, tana kuma maraba da zuwan kamfanonin kasashen waje wadanda ke son zuba jari a kasar Sin. Wannan manufa, a cewar ministan, ta dace da yanayin duniya na samun dunkulewar tattalin arziki.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China