Cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin, da hadin gwiwar kamfanin nazarin alkaluma na Clarivate Analytics, sun fitar da wani rahoto kan aikin nazarin kimiyya da fasaha a duniya na shekarar 2016 a jiya Litinin, inda rahoton ya nuna cewa, kasar Sin ta kasance kan gaba, a fannin nazarin wasu bangarori 30 cikin bangarori 180 na kimiyyar da ta shafi halittun duniya, da ma rayuwar dan Adam, da sauran sassan ilimi, wadanda aka fi mai da hankali a kansu. Wannan bincike ya nuna cewa, kasar Sin ce ke biye da kasar Amurka a matsayi na biyu, a fannin jagorantar mafi yawan bangaraorin ilimin da ake nazari a kansu a dukkanin fadin duniya. (Bello Wang)