in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na son hada kai da kasashen Afirka wajen yaki cutar AIDS
2016-11-01 20:44:00 cri

Yau Talata ne, a nan birnin Beijing, Madam Peng Liyuan, uwar gidan shugaban kasar Sin ta gana da madam Gertrude Mutharika, uwar gidan shugaban kasar Malawi kuma mataimakiyar shugabar kungiyar matan shugabannin kasashen Afirka da ke yaki da cutar AIDS.

A yayin ganawar tasu, madam Peng ta ce, kasar Sin tana son musayar kyawawan fasahohin yaki da cutar AIDS da kasashen Afirka ciki had da Malawi. Haka kuma kasar Sin tana son inganta cudanyar juna a tsakaninta da kungiyar matan shugabannin kasashen Afirka da sauran kungiyoyin shiyya-shiyya ta fuskar yaki da cutar AIDS, a kokarin ba wa kasashen Afirka goyon baya a fannonin yaki da cutar AIDS da kiwon lafiyar al'umma gwargwadon iyawarta. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China