in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta inganta hadin gwiwa da kasashe masu magana da harshen Portugal
2016-10-11 17:13:42 cri

A safiyar Talatar nan 11 ga wata ne aka bude taron ministoci, na dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashe masu magana da harshen Portugal, ta fuskar tattalin arziki da ciniki karo na 5 a yankin musamman na Macao dake kasar Sin, inda firaministan kasar Li Keqiang ya gabatar da jawabi.

A cikin jawabin nasa, Li Keqiang ya ce wajibi ne a inganta amincewar juna tsakanin kasar Sin da kasashe masu magana da harshen Portugal ta fuskar siyasa, a kuma kara azama kan zuba jari, da gudanar da ciniki cikin 'yanci kuma cikin sauki. Har wa yau ya dace a habaka hadin gwiwa ta fuskar kera kayayyaki, da kara bunkasa mu'amalar al'adu, a kokarin samar da misali mai kyau a fannin hadin gwiwar abokantaka a tsakanin kasashe.

Har wa yau, firaministan kasar Sin ya sanar da sabbin matakai 18 da gwamnatin Sin za ta dauka, domin kyautata hadin gwiwa a tsakaninta da kasashe masu magana da harshen Portugal nan da shekaru 3 masu zuwa, ciki hadda bai wa kasashe masu magana da harshen Portugal na Asiya da Afirka tallafi, da kuma tura musu likitoci, da samar wa kasashe mambobin dandalin damar samun horaswa da kudin yabo na karatu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China