in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da shugabanni dake halartar dandali tsakanin Sin da kasashe masu amfani da Portuguese
2016-10-11 11:00:33 cri
A yammacin jiya ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da firaministan kasar Guinea-Bissau Baciro Dja dake halartar taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da kasashe masu amfani da harshen Portuguese a birnin Macao dake kasar Sin.

A yayin ganawar, Li Keqiang ya bayyana cewa, Sin tana girmama hanyar samun bunkasuwa da ya dace da jama'ar kasar Guinea-Bissau suka zaba, tana kuma fatan kiyaye mu'amala a tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu, tare da nuna imani da juna a fannin siyasa, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu.

Mr Li yana fatan kasar Guinea-Bissau za ta yi amfani da damarta ta kasancewa kasa mai amfani da harshen Portuguese, da dandalin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na birnin Macao, da shigar da albarkatunta zuwa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen dake yankin yammacin Afirka da kasar Sin, wadannan za su taimaka wajen samun bunkasuwa tare da amfanawa jama'arsu.

A nasa jawabin, Baciro Dja ya bayyana cewa, Sin ta baiwa Guinea-Bissau goyon baya da gudummawa yayin da ta ke kokarin samun 'yancin kai, tare da taimakawa a fannin bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar, da ba da taimako ga kasashen Afirka ba tare da gindaya wani sharadi ba. Kasar Guinea-Bissau tana yiwa kasar Sin godiya, da yin imani ga makomar hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu. Haka kuma kasarsa tana son kiyaye mu'amalar manyan shugabannin kasashen biyu, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu a harkokin kasa da kasa bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, da dandalin tattaunawar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da kasashe masu amfani da harshen Portuguese, da taimakawa raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kungiyar ECOWAS, da kasashe masu amfani da harshen Portuguese da kasar Sin gaba daya.

Bugu da kari, Li Keqiang ya gana da firaministan kasar Cape Verde José Ulisses Correia e Silva da na Mozambique Carlos do Rosário wadanda suke halartar taron dandalin tataunawar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China