in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Peng Liyuan ta halarci bikin bude tawagar hadin gwiwa ta yaran Sin da Afirka ta shekarar 2016
2016-07-30 12:53:27 cri

An gudanar da bikin bude tawagar sada zumunta ta yaran Sin da Afirka ta shekarar 2016 a jiya Juma'a 29 ga wata a tsohuwar fadar sarki Summer Palace dake nan birnin Beijing, inda matar shugaban kasar Sin kuma wakiliyar musamman ta hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO mai kula da rigakafi da yaki da cutar tarin fuka da AIDS Madam Peng Liyuan ta halaci bikin. A cikin jawabinta, Peng Liyuan ta bayyana cewa, kulawa da yara masu fama da cutar AIDS shi ne wani babban nauyi dake kan al'ummar kasa da kasa, don haka ana bukatar karin mutane ko hukumomi wajen shiga wannan aiki.

Tawagar sada zumunci, tawaga ce da kungiyar rigakafi da yaki da cutar AIDS ta kasar Sin ta kafa don kulawa da yara masu fama da cutar AIDS. Kuma wannan shi ne karo na shida tun bayan kafuwar tawagar a shekarar 2010.

A matsayin wakiliyar musamman ta hukumar WHO mai kula da rigakafi da yaki da cutar AIDS, Peng Liyuan ta taba halartar wannan aiki har sau 5 a baya. A gun bikin budewar tawagar a wannan karo a ranar 29 ga wata, Peng Liyuan ta bayyana cewa, a wannan karo, an gayyaci yara daga kasashen Afirka a karon farko, don haka tana fatan wadannan yara za su bude ido da sada zumunta da kuma fara son kasar Sin ta hanyar wannan aiki. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China