Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan yayin wani taro game da yi wa rundunar sojojin kasar gyaran fuska wanda aka gudanar daga ranar 24 zuwa 26 ga wata, ya kuma lashi takwabin ganin sassan sojojin kasar na tafiyar da harkokinsu kamar yadda dokoki da tsare-tsaren aikin soja suka tanadar.
Xi ya ce, kamata ya yi a tanadi tsarin da zai baiwa hukumar koli mai kula da harkokin sojojin kasar 'yancin tafiyar da harkokin mulki da yadda za ta jagoranci rundunar sojan 'yan tar da jama'a ta kasar Sin.
Ya ce hakan zai ba da damar kirkiro shiyoyin tunkarar abokan gaba. Kana ana sa ran kwamandojin sojojin su mayar da hankali kan yadda za su inganta ayyukansu.
Manufar yiwa rundunar sojojin kasar gyaran fuska ita ce kara inganta ayyukan dakarun kasar. (Ibrahim Yaya)