in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu kafofin watsa labaran Najeriya
2016-10-25 19:13:27 cri
Masu ruwa da tsaki sun fara bayyana damuwa game da umarnin da babban bankin Najeriya ya bayar, na dakatar da raba ribar hannayen jarin kamfanin sadarwa na MTN daga ribar da kamfanin ke samu a cikin kasar, bayan da bankin ya zargi MTN da safarar kudade daga kasar ta barauniyar hanya.

Masu mallakar hannayen jarin kamfanin dai sun bayyana cewa wajibi ne a raba irin wannan riba ga masu ita, muddin dai an riga an bayyana samuwar ta. (The Guardian)

Hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arziki ta'annati a Najeriya EFCC, ta tsare tsohon ministan birnin tarayyar Najeriya Sanata Bala Mohammed. Kaza lika EFCCn ta damke kakakin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, wato Reuben Abati, bisa zargin almubazzaranci da kudin hukuma. (Daily Trust)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China