in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu kafofin watsa labaran Najeriya
2016-10-24 19:17:57 cri
Rahotanni na cewa sashen zartaswa da bangaren majalissar dokokin Najeriya sun saba, game da kasafin kudin shekarar 2017 mai zuwa. Majalissar dattawan kasar dai ta dakatar da aiki kan kasafin kudin kasar na matsakaicin lokaci ko (MTEF), da kuma tsarin kashe kudade na (FSP).

Majalissar ta kuma gayyaci ministan kasafin kudi da tsare tsare Udoma Udo Udoma, da kuma ministar kudin kasar Kemi Adeosun domin jin a bakin su game da wasu sassa na kasafin kudin. (The Guardian)

Kalubalen tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta yanzu haka na ci gaba da yin tasiri a sassa da dama, inda wata majiya ke cewa kamfanin hamshakin dan kasuwar nan dan Najeriya Aliko Dangote, ya sallami mutane 48 daga aiki.

Wata majiya ta tabbatar da cewa cikin wadanda aka sallama hadda 'yan kasashen waje 36 da kuma 'yan kasar su 12. Ma'aikatan da korar ta shafa dai na aiki ne a helkwatar kamfanin da kuma daya daga kananan rassan sa. (The Punch)

Mafarauta dake agazawa dakarun sojin Najeriya sun dakile wani hari da wasu mahara suka kaiwa kauyen Madagali dake jihar Adamawa, a arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da kuma ya sabbaba kisan maharan su 7. (Daily Trust)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China