in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga kafofin watsa labaran Najeriya
2016-10-26 19:03:57 cri
Karamin ministan ma'aikatar makamashi, ayyuka da gidaje a tarayyar Najeriya Mustapha Baba Shehuri, ya ce za a kammala aikin samar da lantarki, ta sabuwar madatsar ruwan Mambilla nan da watannu 63.

Shehuri wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, yayin da ake kaddamar da cibiyar kamfanin gine gine na kasar Sin CGCC ta arewa maso yammacin Afirka a birnin Abuja, ya yaba da kwazon kamfanin, wanda ya ce bayan kammalar aikin madatsar ruwan, zai samar da wutar lantarki da ta kai megawatt 3,050. (Daily Trust)

Hukumar EFCC ta sha alwashin ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, don haka ne ma hukumar za ta ci gaba da sanya ido kan alkalan kasar, da ma sauran masu ruwa da tsaki a fannin shari'a.

Shugaban hukumar Ibrahim Magu ne ya bayyana hakan, yana mai cewa sabanin ra'ayoyi da aka ci karo da shi, sakamakon kama wasu alkalan kasar a kwanakin baya, ba zai sanyaya gwiwar hukumar, wajen gurfanar da jami'an sashen shari'ar da ake zargi da karya dokar kasar ba.

(The Guardian)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China