Bankin duniya da asusun ba da lamuni na duniya (IMF) sun matsawa gwamnatin Najeriya lamba kan ta zayyana tsare-tsarenta na tattalin arziki, muddin tana bukatar rancen kudaden da ta ke son karbowa daga katera.(Vanguard)
Dubban jama'a a sassa daban-daban na Najeriya ne ke yin tururuwa zuwa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a kowa ce rana, sakamakon zazzabin cizon sauro ko Malaria da ake fama da shi.
Rahotanni daga jihohin kasar na cewa, cutar ta yi sanadiyar rayuwan mutane da dama. Yanzu haka masu fama da cutar da dama ne ke amfani da maganin gargajiya, saboda matsalar kudi ko cunkuson a asibitocin.(Daliy Trust)