A jiya Talata ne ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin Alkahira, hedkwatar kasar Masar ya shirya liyafar murnar cika shekaru 67 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin.
A jawabinsa yayin liyafar, jakadan kasar Sin dake kasar Masar Song Aiguo ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya tare da sauran kasashe. A shekarun baya, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ba tare da tangarda ba ya inganta farfadowar tattalin arzikin duniya. Musamman ma, yadda kasar Sin ta yi kira da a raya tattalin arziki ta hanyar kirkiro sabbin kayayyaki da yin hadin gwiwa tare da sauran kasashe da kuma cimma daidaito a tsakanin kasa da kasa a gun taron koli na G20 da aka yi a farkon wannan wata a birnin Hangzhou na Sin, ya samu amincewa sosai daga kasashen duniya. Ba ma kawai kasar Sin ta ba da gudummawa wajen inganta ci gaban tattalin arzikin duniya ba, hatta ma ta gabatar wa duniya irin matakan da ta yi amfani da su wajen raya tattalin arzikinta.(Lami)




