in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar EU da Canada sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa
2016-10-31 11:20:22 cri
Kungiyar hadin kan turai ta EU da kasar Canada, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna, wadda za ta basu damar kara inganta dadaddiyar dangantakar su.

Sassan biyu sun cimma hakan ne dai a yayin taron mahukuntan EUn da kasar Canada, wanda ya samu halartar firaministan kasar Canada Justin Trudeau a jiya Lahadi.

Wata sanarwar bayan taron ta bayyana cewa, yarjejeniyar za ta shafi fannin fadada alakar siyasa, da tsaro, tare da burin wanzar da zaman lafiya da lumana. Sauran sun hada da inganta harkokin shige da fice, da yaki da ta'addanci, da samar da makamashi, da batun sauyin yanayi, da bincike tare da kirkire kirkire, baya ga batun bunkasa ci gaban juna.

Kaza lika sanarwar ta jaddada aniyar mahukuntan sassan biyu, na aiwatar da daukacin sassan yarjejeniyar Minsk, wadda ta shafi kawo karshen sabani game da kasar Ukraine, tana mai kira da aka kai zuciya nesa, a kuma tabbatar da warware takaddamar ta hanyar lumana.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China