Kwamitin tarayyar Turai ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa wannan sabon taimakon kudin ya zo bayan tashe tashen hankalin Boko Haram a arewacin Najeriya da suka janyo zaman dar dar sosai a shiyyar tafkin Chadi, tare da janyo gudun hijira na miliyoyin mutane.
Wannan karin taimakon kudade na EU zai mai da hankali kan taimakon gaggawa, musamman ma a fannonin abinci da abinci mai gina jiki, ruwan sha da kuma tsabta, da ma kiwon lafiya. Ya kamata a aiwatar da dukkan kokari domin tabbatar da ganin cewa shirye shiryen ayyukan jin kai sun isa ga wadanda dake cikin bukatar gaggawa, in ji kwamishinan tarayyar Turai mai kula da agajin jin kai da kula da bala'u, Christos Stylianides. (Maman Ada)