Kafin bude taron a wannan rana, babban sakataren NATO Jens Stoltenberg, da shugaban majalisar Turai Donald Tusk, da shugaban kwamitin EU Jean-Claude Juncker sun sa hannu kan hadaddiyar sanarwa, inda suka tsaida kudurin karfafa hadin kai tsakanin wadannan manyan kungiyoyi.
Sanarwar ta ce, NATO da EU suna kasancewa muhimman abokan hadin kai ga juna, yanzu suna bukatar karfafa hadin kansu don tabbatar da tsaro a Turai da kuma sauran yankuna, tare kuma da taimakawa kasashe makwabtaka da sauran abokai wajen tabbatar da zaman karko.
A lokacin hutu na taron kolin din kuma, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi ganawa da shugabannin EU Donald Tusk, da Jean-Claude Juncker, inda bangarorin biyu suka bayyana cewa, za su kara hadin kai don tinkarar kalubalen janyewar Burtaniya daga EU, da kuma sauran matsaloli. (Bilkisu)