An gudanar da bikin mika tallafin ne a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya, WFP ta yabawa gwamnatin Sin bisa wannan namijin kokari.
Daraktan shirin WFP dake Somali Laurent Bukera, ya ce za'a yi amfani da kudaden tallafin da kasar Sin ta bayar wajen samar da abinci mai gina jiki ga yara kanana, da mata wadanda ke fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki.
Jakadan kasar Sin a Somaliya, Wei Hongtian, ya fada a lokacin bikin cewa, "kasar Sin tana ci gaba kuma za ta ci gaba da kasancewa babbar aminiya kuma mai taimakawa gwamnatin Somaliya da hukumomin MDD, ciki har da shirin hukumar WFP.
Ministan cikin gidan Somaliya Abdurashid Muhamed Hidig, ya yabawa gwamnatin kasar Sin a madadain gwamnatin kasar Somaliya, ya kara da cewa gwamnatin kasar Sin da alummar Sinawa sun jima suna bada taimako wajen cigaban kasar Somaliya. (Ahmad)