in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taro game da ayyukan tawagar AMISOM
2016-10-21 10:35:12 cri
A jiya Alhamis ne aka kammala taron yini biyu game da zakulo hanyoyin inganta ayyukan tawagar wanzar da zaman lafiya mai aiki a kasar Somaliya.

Mahalarta taron dai sun maida hankali ga nazarin dabarun hadin gwiwa tsakanin sassan masu ruwa da tsaki a ayyukan tawagar ta AMISOM. Sassan sun kunshi bangaren sojoji da fararen hula, tare da jami'an wanzar da zaman lafiya masu tallafawa samar da agajin jin kai.

Kaza lika an tattauna game da tsare tsaren da aka tanada, don gane da ayyukan hadin gwiwa tsakanin AMISOM da sauran hukumomin dake aikin jin kai a kasar.

Masana na ganin ya zama wajibi a kara kwazo wajen tattaunawa, da nufin tunkarar kalubalolin dake fuskantar ayyukan AMISOM, dama na sauran masu bada agaji dake aiki a Somaliya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China