in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
HCR: Fiye da 'yan gudun hijirar Somliya dubu 33 dake Kenya sun koma kasaru bisa son rai
2016-10-23 12:36:28 cri
Babbar hukumar dake kula da 'yan gudun hijira ta MDD (HCR) ta sanar a ranar Asabar cewa fiye da 'yan gudun hijirar Somaliya dubu 33 da suka kaura a Kenya suka bar sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab dake gabashin Kenya domin komawa kasarsu tun cikin watan Disamban shekarar 2014 bisa son ransu.

A jimilce, zuwa ranar 15 ga watan Oktoba, 'yan gudun hijirar Somliya dubu 33 da 178 suka koma kasarsu bisa son ransu tun daga ranar 8 ga watan Disamban shekarar 2014, wato ranar da hukumar HCR ta fara bada kwarin gwiwa ga komawarsu gida bisa son rai, wanda kusan dubu 27 da 77 a shekarar 2016 kawai, in ji hukumar MDD a cikin wani rahoto.

Rahoton ya jaddada cewa 'yan gudun hijira 517 an kwashe ta jirgin sama a wadannan makwanni biyu na baya baya, tare da bayyana cewa an sake bude jigila ta hanyar jiragen sama zuwa sau uku a kowane mako.

Bisa dalilin dakatar da karbar ayarin motoci daga bangaren hukumomin Jubaland dake kudancin Somaliya, ayyukan sun fara saukaka dawowa zuwa Baidoa ta hanyar jirgin sama, in ji HCR.

A cewar MDD, wadannan ayarin motoci an dakatar dasu tun a ranar 30 ga watan Agustan da ya gabata bayan da hukumomin wannan yanki mai cin gashin kansa mai iyaka da Kenya suka sanar da HCR cewa ba za su amincewa da wadannan ayyukan dawowar 'yan gudun hijira ba idan har ba za a warware batun shirin dunkulewa a Somaliya ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China