in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara zaben karamar majalisar dokokin kasar Somaliya
2016-10-25 09:46:59 cri
Hukumar zaben kasar Somaliya ta ce ba za ta tsawaita wa'adin zaben kujerun karamar majalisar dokokin kasar ba wanda aka fara tun a ranar Lahadi, duk da irin hasashen da wasu ke yi na yiwuwar fuskantar hargitsi.

Omar Muhammad Abdulle, shi ne shugaban hukumar zartaswa ta tarayya na hukumar zaben kasar, ya fada cikin wata sanarwa cewa, za'a kammala zaben karamar majalisar ne zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba.

Bayan an kammala zaben majalaisun dokokin biyu, sabbin 'yan majalisun da aka zabe ne za su zabi shugaban kasar a ranar 30 ga watan Nuwamba.

Ya kara da cewa, ana sa ran za'a cimma kudirin baiwa mata kaso 30 cikin 100 na kujerun majalisar dokokin kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China