in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin gwamnatin Libiya ya tabbatar cewa al-Theni na kan mukaminsa na firaminista
2015-08-14 11:11:07 cri
Kakakin gwamnatin kasar Libiya da gamayyar kasa da kasa ta amince da ita, ya bayyana a ranar Alhamis cewa faraminista Abdallah al-Theni na nan kan mukaminsa, kwana guda bayan sanarwar da ya bayar ta yin murabus.

Firaminista da gwamnatinsa za su ci gaba da tsaya wa kan aiki,kuma gwamnatin ba za ta yi murabus ba, in ji kakakin gwamnatin Libiya, Hatem Oaribi, tare da cewa gwamnati ta tsaya a shirye domin bayyana a gaban majalisar dokoki inda za ta sake jaddada nauyin da ke wuyanta a kowa ne lokaci.

A ranar Laraba, mista Theni ya sanar a yayin wata hira da wani gidan talabijin mai zaman kansa na kasar Jordan cewa zai sauka daga mukaminsa, bayan an soki fadarsa da kasa tabuka kome wajen warware matsalolin Libiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China