in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dage kaddamar da sabuwar gwamnatin kasar Libiya
2016-01-18 11:12:22 cri
Majalissar shugabancin kasar Libiya, ta sanar da dage kaddamar da sabuwar gwamnatin hadin kan kasar da kwanaki biyu domin kammala wasu muhimman tsare tsare.

A ranar 17 ga watan da ya gabata ne dai sassan kasar da ba sa ga maciji da juna, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen rabuwar kai karkashin inuwar MDD, tare da hada gwiwa domin yaki da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi, da kuma barazanar da kungiyar IS ke yi ga kasar.

Yarjejeniyar ta tanaji kafa sabuwar gwamnatin ne cikin kwanaki 30, sai dai kuma a daya bangaren masu tsattsauran ra'ayi daga dukkanin sassan kasar biyu sun yi fatali da sakamakon yarjejeniyar.

A jiya Lahadin ne kuma shugaban tawagar wanzar da zaman lafiyar MDD a Libiya Martin Kobler, ya ja hankalin majalissar shugabancin kasar, game da muhimmancin zartas da kudurin kafa sabuwar gwamnatin ta hadaka, yana mai cewa dage lokacin kaddamar da gwamnatin wani abun takaici ne.

Kasar Libiya dai ta tsunduma cikin halin rudani ne tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Gaddafi a shekarar 2011. Kawo yanzu kasar na karkashin gwamnatoci biyu masu adawa da juna, yayin da kuma ake ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula, da hare-hare daga kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi dake dauke da makamai. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China