Kwanan baya ne, mataimakin shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo ya gana da shugabannin kamfanonin kasar Sin 2 da wasu jami'an ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke kasar a fadar shugaban kasar da ke Abuja.
A yayin ganawar, Osinbajo ya yi maraba da shugabannin kamfanonin kasar Sin 2 da hannu bibbiyu. Yana mai da cewa, gwamnatin Najeriya tana ba da muhimmanci game da raya hulda a tsakaninta da kamfanonin kasar Sin, sakamakon yadda hadin gwiwar da ke tsakanin sassan 2 za ta taimakawa gwamnatin Najeriya matuka. Ya kuma jaddada cewa, gwamnatinsa tana kara azama wajen kera kayayyaki a kasar, don haka tana son inganta hadin kai da kamfanonin kasar Sin, musamman ma a fannin fasahar zamani, a kokarin raya aikin kera kayayyaki a kasar ta Najeriya.
Shugabannin wadannan kamfanonin Sin guda 2 sun ziyarci kasar Najeriya ne bisa gayyatar mista Chukuma Innocent Ifediaso, shugaban kamfanin Innoson, kana shugaban masu masana'antu da 'yan kasuwa na Najeriya.
Sun fara ziyarar tasu ce a ranar 24 ga wata, inda suka yi rangadi a fannin kulla hadin gwiwa tsakanin kafofin yada labaru, dangane da yadda za su kulla yarjejeniya a fannin watsa shirye-shiryen telibijin na zamani. (Tasallah Yuan)